wasu irin kudade ne wadanda ake amfani dasu a internet kawai. Ana amfani dasu sabanin na takarda, kuma wadannan kudade ba'a iya ganinsu a zahiri ballantana ma a tabasu.
BITCOINS shine mafi suna da karbuwa a kudaden cyptocurrency, don a yanzu babu wani irin abun kudi da ya kai darajarsa, kamar irinsu Gwal, Diamond, Saboda duk bitcoins daya ana iya sayar dashi sama da $17,000 wanda a yanzu yayi dai-dai da N6,120,000.
BITCOINS: An samar dashi a shekarar 2009, wanda ya samar dashi shine SATOSHI NAKAMOTO.
Mining: Mining wata hanya ce da za'a iya samun Bitcoin ta hanyar bawa computer dama ta shiga tsare-tsaren sarrafa milyoyin bayanai da ake samarwa game da Bitcoin a (Internet). Wannan shine zai bawa mutum damar samun Bitcoin dai-dai da yawan bayanan da wannan computer ta sarrafa. Amma wannan hanyar tana da wuya sosai domin karamar computer (mini) ba zata iya yin wadannan aiyukan ba.
Buy: Hanya ce ta sayen wannan bitcoin daga dullalan sa.
Akwai shafuka da dama a internet da suke harkar dillancin Bitcoin.
Su wadannan shafuka kamar banki suke, inda ake ajiye su kamar sauran bankuna da muka sani, suma wadannan shafuka suna baiwa mutum dama ne ya bude account na bitcoins a cikin website dinsu. Wannan account da ake ajiyar kudin Bitcoin shi ake kira da Wallet.
Idan kuma mutum na da bukatar siyar da Bitcoin dinsa, to wadannan shafukan zasu iya siya daga gareshi.
Amma fa a kula sosai wajen tantance sahihan dillalan Bitcoin domin akwai wasu ‘yan yaudarar mutane akan irin wadannan harkokin.
No comments:
Post a Comment